ميثاق علماء الأمة (اللغة الهوساوية)

    

Matsayin Malaman Musulunci A kan

Sasantawa da Yahudawa:

Wajabcin  Kalubalantar Wannan Siyasa

1.0 Shimfida:

Dukan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Madaukakin Sarki shi kadai. Tsira da aminci su tabbata ga Annabin nan da babu wani Annabi bayansa. Bayan haka. Tabbatacciyar magana ce, cewa babu wani musulmi da yake nunfashi a bayan kasa; fadin gabas da yammacin duniya, face yana da imanin cewa, gwagwarmaya domin kwato wuraren ibadar Musulunci da suke kasar Falasdinu daga hannun Yahudawan duniya, al’amari ne da ya sadaukantar da rayuwarsa a kai, a matsayinsa na wani nauyi da Allah Madaukakin Sarki zai tambaye shi a gobe Kiyama.

Sai ga shi kuma, tattare da abubuwan da suka faru na tsawon tarihi a kan wannan al’amari. An wayi gari yau, wani tsari da yake gudanar da sha’anin siyasa a matakin duniya, yana kokarin tilastawa tare da kawo wani shiri da zai tabbatar da wani abu wai shi  “sasantawa” tsakanin Musulmi da Yahudawan Duniya, wanda a karshe zai tilasta wasu musulmin yin watsi da gwagwarmayar kwato wannan kasa tasu tare da tarwatsa waccan akida da take cikin jininsu ta ‘yanto Kudus tare da yi mata wankan tsarki daga kazantar Yahudawa ‘yan fashi da makami kuma ‘yan kama-wuri-zauna. Bayan sun kuma kankare wannan akida daga zukatan ‘ya’yan Musulmi, su kuma tilasta musu zama Yahudawan karfi da yaji.

To, bisa la’akari da fadar Allah Madaukakin Sarki: “Lalle ne ku bayyana shi ga mutane kuma ba za ku boye shi ba” (Ál-Imran:187). Da kuma aiki da umarnin Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam, kamar yadda Imamu Muslimu da waninsa suka riwaito, cewa: “Addini nasiha ne.”  Bisa wannan tubali ne, wani jerin gwano na malaman Musulunci daga lunguna da sako-sako na sasannin duniya suka hadu, domin fayyace hakikanin gaskiyar hatsarin da wannan sasantawa take kunshe da shi, a matsayin tasu nasiha. A karshe kuma su karfafa goyon bayansu ga matsayin da malaman Musulunci suke a kai, wanda ba a taba samun wani lokaci da suka saba wa juna a cikinsa ba, wato, wajabcin yin fito-na-fiti da wadannan Yahudawa ‘yan fashi da makami ‘yan kuma kama-wuri-zauna, ta hanyar amfani da duk wata hanya wadda ba ta saba ma Shari’a da doka ba.

Bayan taruka na ilimi da shawarwari a kan tanade-tanaden Shari’a da yin ido kifi ido bado tsakanin wadannan abubuwa guda biyu da kuma abin da yake faruwa a wannan iska da yake kadawa. Gaba dayan malaman da suka halarci wadannan taruka, sun yanke hukunci, ba tare da la’akari da wurare da kungiyoyi da ma’aikatun da suka fito ba, ko matsayin da suke da shi a cikin al’umma. Sun yanke hukuncin cewa, wannan sasantawa da dukan abin da ta kunsa, na siyasa da tattalin arziki, da al’adu da sauran lissafe-lissafe, ta yi ban hannun makaho da Shari’a da doka; ta kuma fada cikin rukunin miyagun abubuwan da taka musu birki da ganin baya gare su tare da yi wa duniya hannunka-mai-sanda a kan su, yake wajibi. Saboda haka ba ya halasta ga wata kasa ko jam’iyyar siyasa ko kungiya da take gwagwarmayar yakar wannan zalunci, ta yarda balle ta amince da wannan shiri, ko mika kai bori ya hau. Babbar madogara a kan wannan kira kuwa shi ne fadar Allah Madaukakin Sarki: “Allah yana hana ku kawai daga wadanda suka yake ku saboda addini, suka kuma fitar da ku daga gidajenku, suka kuma taimaki juna ga fitar da ku, kar ku jibince su. Wanda kuma ya jibince su, to, wadannan su ne azzalumai.” (Mumtahana:9)

Wannan yana tabbatar da cewa, babu abin da yake wajaba a kan musulmi illa yin fito-na-fito da wannan karen aiki ta hanyar duk da yake iyawa. Yin haka kuwa tabbatar da zaman sa ne daya daga cikin masu biyayya ga umarnin Annabi sallallahu alaihi wa sallam da ya ce: “Duk wanda ya ga wani mugun aiki daga cikinku, to, ya hana shi da hannunsa. Idan ba shi da ikon yin haka, to, ya yi amfani da harshensa. Idan kuma haka din ma ta faskara, to, sai ya kyamaci abin a zuciyarsa. Wannan shi ne mafi raunin imani.” (Muslim ne ya riwaito shi).

Da wannan matsayi kuma da wadannan malamai suka dauka, suna yin tunatarwa ne musamman, ga shugabannin musulmi da sauran fararen hula a duniyar Musulunci, a kan nauyin da Shari’a ta dora musu na mikewa tsaye tsayin daka, don ganin sun ‘yanto wannan kasa ta Musulmi tare da kare mutunci da alfarmar mutanen da suke cikin ta, da kuma diyauta wuraren ibadarta masu tsarki. Haka kuma malaman, suna kara tabbatarwa ne, tare da fitowa fili karara, da cewa yin fito-na-fito da wannan siyasa ta sasantawa, nauyi ne da gaba dayan addinan da Allah Madaukakin Sarki ya saukar, da sauran dokoki da yarjeniyoyi da tanade-tanaden al’adun kasashen duniya, suka dora a kan ‘ya’yan Adamu. Siyasa ce wadda, babu wata lalura ko bukatar rayuwa ta wajibi, da suke iya halastawa, ko bayar da damar tabbatarwa. Babu kuma wani yanayi na rayuwa da yake wakana a wani kebantaccen lokaci, da yake daure wa hakan gindi.

To, domin kokarin dauke nauyi da kubutar da kai, tare da yi wa gaba dayan al’ummar musulmi gargadi da hannunka mai sanda a kan wannan musiba da danyen aiki na sasantawa da Yahudawa ‘yan fashi da makami, da aka sha damarar yi. Nauyi wanda manyan malamai kwararru daga kasashe da fannonan ilimi daban-daban, suka yi tarayya a cikin daukewa, aka samar da wannan yarjejeniya a matsayin wani matani na Kundin Gudanarwa, wanda zai zama jagora ga malaman wannan al’umma, na mu’amala tsakanin ta da wannan shiri na sasantawa da Yahudawa, da matakan da za su dauka a cikin kalubalantar sa. Walláhu yaqúlul haqqa wahuwa yahdis sabil.

Bayanai da Ja-makafi:

  1. Kalmar Mithaq; Alqawari da muka yi amfani da ita a cikin wannan bayani tana nuni zuwa ga wasu tuwasu da wasu hukunce-hukuncen Shari’a waxanda Malaman al’umma da suka sanya hannu akan tad a manufar bayanin hukuncin Shari’a a kan sasantawa da Yahudawa da Suhuyuniyawa tare da bayanin abinda Shari’a ta wajabta a kan haka.
  2. In da muka yi maganar Suhuniyawa muna nufin wasu yan kama wuri zauna da suka yi ka-ka-gida a qasar Falasxinu, suka qwace qasar daga masu ita, suka wulaqanta wurare masu tsarki, suka keta alfarmar ‘yan qasar tare da cin zalun su.
  3. In da muka yi maganar sasantawa da Yahudawa muna nufin gyara hulxa da Suhuyuniyawa ta fuskar da za ta cuta ma masu neman yancinsu daga hannunsu ko ta hanyar da za a nuna amincewa da wannan qwacen na zalunci da suka yi ma qasar Falasxinu tare da wulakanta alfarmarta.

Manufofin Sasantawar da na Masu Ita:

  • Ba komai Yahudawa suke nufi da wannan sasantawa ba, illa lulluba wa yunkurin da suke yi na tabbatar da wanzuwa, rigar halascin Shari’a, wanda hakan zai kara tsattsage turakun tafiyar tasu tare da tabbatar da samuwarta, daram, a matakin cikin gida da na waje. Hakan kuma zai lamunce wa wannan yunkuri nasu cikakkiyar damar fadada da girma da bunkasa, da samun cikakken ikon danne alummar musulmi da kwace mata ‘yanci da duk wani iko da take da su.
  • Ita kuwa moriyar da wadanda suke fafutukar shimfida tabarmar wannan sasantawa da kungiyar Yahudawa, suke ganin musulmi za su samu, moriya ce wadda ba ta da gurbi a idon Shari’a. Ba kuwa don komai ba, sai don kasancewarta guradau; cinikin kifi ruwa, babu tabbas a cikin samuwarta. Sa’annan kuma matsaloli da bala’o’in da take tattare da su zuwa ga Falasdinawa da sauran al’ummar musulmi, Allah kadai ya san iyakarsu. Moriya ce wadda darussan da al’ummar musulmi suke da su, na abubuwan da suka faru a baya na tarihi, da wadanda suke faruwa a yau, da alamomin wadanda za su faru nan gaba, duk sun karyata yiwuwar samuwarta.

Matsayin Kungiyar Yahudawa Da Hukuncinta a Shari’a da Doka:

  • Wannan babbar kungiya ta Yahudawa haramtacciyar kungiya ce a idon Shari’a, saboda manufofin da take tafiya a kan su na mamaya da fashi da makami a kan gidaje da wuraren ibada, da tozarta addini da rayuwa da hankali, da dukiya da zuri’a na wadanda ba su ba. Kalubalantar irin wannan ta’addanci kuwa tare da yin fito-na-fito da shi, wajibi ne a idon Shari’ar Musulunci.
  • A idon kagaggun dokoki kuwa, wannan kungiya ta Yahudawa, ba ta da dalilin samuwa balle gindin zama. An dai samar da ita ne kawai sakamakon fin karfi da ta’addaci. Saboda haka kuwa kalubalantar ta, ko da ta hanyar daukar makami ne, hakki ne da yake da gurbi a cikin kagaggun dokokin kasa-da-kasa da al’adunsu.
  • Duk kuma wasu dokoki da hukunce-hukunce da suka tuzgo a matakin kasa-da-kasa domin halastawa da samar wa mamayar da wannan kungiya ke yi gindin zama, dokoki ne na banza a idon Shari’a, a yayin da su kuwa kagaggun dokoki ba su ma san da zamansu ba.

Hukunce-hukuncen Shari’a da na Dokoki a Kan Wannan Sasantawa:

  • Sasantawa da Yahudawa din nan haramun ne a idon Shari’a, saboda irin yadda hakan take takin saka da sharuddan imani da ka’idojinsa, wadanda suka tanadi wajabcin rayuwa kafada da kafada da sauran muminai kamar tsintsiya mai madauri daya, da kuma ba su agaji da taimako da gudunmawa a duk lokacin da suka bukata. A hannu daya kuma ya wajabta raba jaha da duk wanda yake zaluntar su, tare da toshe duk wata kafa ta musayar soyayya da kauna da ‘yan’uwantaka zuwa ga irin wadannan makiya da suka fitar da musulmi daga gidajensu, suka kuma raba su da wuraren ibadarsu masu tsarki.
  1. Haka kuma duk wata yarjejeniya da fahimtar juna, wadanda aka daddale da Yahudawan nan, da sauran rassan abubuwan da suka rataya da hakan na wajibi, duk, haramtattu ne a idon Shari’a, da babu wani tasiri tare da su; bakin banza suke da wofi. Saboda haka haramun ne a yi wa shugaba biyayya a kan su. Haka kuma ba su da wani gurbi a cikin kagaggun dokoki sakamakon irin yadda suke bayar da damar yin ta’addaci a kan al’umma da sauran kabilun Falasdinawa.
  1. Samuwar wannan kungiya ta Yahudawa a aikace, da kulla wannan sasantawa da wasu daga cikin musulmi a bayyane ko a asirce. Wannan ba zai canza matsayinta a idon hukunce-hukuncen Shari’a da na kagaggun dokoki ba. Haka kuma ba zai kankare wajabcin kalubalanta da yin fito-na-fito da su ba.
  1. Mayarwa tare da damka wa musulmi wasu yankuna na kasar Falasdinu, da mayar musu da wadansu hakkoka nasu, duk, ba zai canza hukunci da matsayin wannan sasantawa a a idon Shari’a da doka ba.
  1. Duk wani yunkuri na lullube matsalar Falasdinu din nan da wani farin kyalle ta hanyar aiwatar da wadansu shirye-shirye na samar wa wasu tsiraru mafaka da mazaunai, ko yahudantar da wuraren ibadar Musulunci da karfi da yaji. Hakan ba zai iya tabbatar wa wannan kungiya da wani hakki ba, ko kankare musu matsayinsu na ta’addanci da mamaya da kama-wuri-zauna. Hasalima hakan shi ne babban dalilin da yake haramta wannan sasantawa.

Abin da Ya Wajaba a Kan Shugaba Musulmi Game da Wannan Sasasantawa:

  1. Babban abin da ya wajaba a kan shugaba Musulmi shi ne kiyayewa tare da tsare martabar addini, da gudanar da harkokin duniya bisa tanade-tanadensa ta hanyar kawar da kowace irin barna da tabbatar da kowane irin alhairi.

Hujjoji da Dalilan Kalubalantar Wannan Sasantawa:

  1. Kalubalantar wannan shiri na sasantawa da Yahudawa abu ne da ya dace da tanade-tanaden da suke kunshe a cikin gaba dayan shari’o’in Ubangiji, da al’adu da kagaggun dokokin kasashen duniya, wadanda suka yanke hukuncin wajabcin yanke kowace irin hulda da ma’amala da kowane irin azzalumi, da kuma yin tsayin daka a hana shi ci gaba da aikinsa na zalunci. A bangare daya kuma, da taimakon wanda aka zalunta har sai an kwato an kuma mayar masa da hakkokansa. Haka kuma;
  1. Kalubalantar wannan shiri abu ne da kyawawan halaye da dabi’u wadanda suka yi kira zuwa ga tabbatar da gaskiya da adalci da karimci da ‘yanci a cikin halin rayuwa, wadanda ’yan Adam masu lafiyayyen tunani suka hadu a kai. Haka kuma;
  1. Kalubalantar wannan siyaya ta sasantawa ba bakon abu ne ba a tarihin wanzuwar dan’ Adam a bayan kasa; gwagwarmaya ce tsakanin gaskiya da bata, da tsakanin alhairi da sharri, da wajabcin taimakon wanda aka zalunta har sai ya samu hakkinsa daga hannun azzalumi.
  1. Kalubalantar sasantawa din nan kuma wata hanya ce daga cikin hanyoyin da wannan al’umma ta musulmi za su bi domin ganin Falasdinu ta samu ‘yancin kanta.

Manufofin Kalubalantar Sasantawar:

  1. Babbar manufar da take tattare a cikin kalubalantar wannan siyasa ta sasantawa da Yahudawa, ita ce kiyaye martabar wannan addini na Musulunci da al’ummarsa, tare da tabbatar masu da cikakken tsaro da kowane irin cigaba, da kuma wanzar da ruhin Musulunci a cikin zukatan ‘ya’yan wannan al’umma da suka kyamaci wannan mamaya.
  • Wata manufar kuma da kalubalantar wannan siyasa take dauke da ita, ita ce kakaba wa yunkurin wannan kungiya ta Yahudawa takunkumi tare da hana masa sakat, da nuna rashin amincewa tare da gurgunta kokarin samar masa gindin zama na dindindin a cikin wannan yanki na Falasdinawa, da saka masa rigar halasci irin na Shari’a. Haka kuma;
  • Kalubalantar wannan siyasa ta sasantawa zai karfafa wa al’ummar Falasdinawa guiwa tare da daga daraja da nauyin irin jajircewar da suke da ita; wani karin gishiri ne a cikin gwagwarmayar da suke yi da neman hakkokansu.

Hadurra da Illolin Wannan Sasantawa:

  • Wannan  shiri na sasantawa da Yahudawa, idan ya tabbata, zai ci gaba da zama wata babbar barazana ga addinin Musulunci da manyan rukunan rayuwar da suka tabbatar da girma da mutuncin dan Adam. Za a wayi gari ‘yanci da adalci da mutunci irin na ‘yan adamtaka, da aminci da zaman lafiya a dakin duniya sun yi ko sama ko kasa.
  • Ko shakka babu, sasantawa da Yahudawa hadari ne babba ga akidar da wannan al’umma take bisa gare ta, ta Musulunci da madaukakin matsayin da wuraren ibadar musulmi suke da shi a cikin zukatan ‘ya’yan wannan al’umma. Babbar barazana ce kuma ga manufofin Shari’ar Musulunci, wadanda suka shafi kiyaye martaba da alfarmar addinin al’umma da rayuwar ‘ya’yanta da dukiya da hankali, da kuma zuri’arsu.
  • Da zarar kuma wannan shiri na sasantawa da Yahudawa ya tabbata, to, hasken waccan fitila na gwagwarmayar kwato ‘yanci, da yake cikin zukatan ‘ya’yan wannan al’umma zai yi rauni ya kuma bice, duhu ya maye gurbinsa.
  • Wannan siyasa ta sasantawa da Yahudawa, za ta zama wani godabe, wanda za su rika amfani da kasashen Larabawa da na Musulunci a kansa, har su shashashantar da maganar ‘yancin Falasdinawa da ganin baya gare ta. A karshe kuma a wayi gari babu wani guri da ya yi saura a cikin zukatan al’ummar Falasdinawa na ‘yanto wannan kasa tasu da dawo mata da gaba dayan hakkokanta,
  • Tabbatacciyar magana ce, cewa babu wata al’umma da za ta zama cikin cikakken aminci, sai idan an wayi gari babu wani rukuni nata, da yake ba cikin aminci ba. Shi kuwa wannan shiri na sasantawa da Yahudawa, wata kofa ce aka buda musu, wadda za su mamaye gaba dayan al’ummar musulmi da ta Larabawa, da karfin soja.
  • Haka kuma wannan sasantawa a matsayinta na wata sabuwar siyasa, za a wayi gari ta hargitsa gaba dayan alkalumman tafiyar al’umma; makiyi ya koma masoyi. Ko shakka babu kuwa, wannan zai haifar da babbar barazana ga zaman lafiyar kasashen Larabawa da na musulmi baki daya.
  • Duk wani yunkuri da kokari da al’ummomin Larabawa da na musulmi suke yi, na kira zuwa ga addinin Musulunci da gyara halayen zaman jama’a, za a wayi gari wannan sasantawa ta siyasa da Yahudawa, ta kai karshensa.
  • Matsayin da al’ummar musulmi suke a kai na sanin ko waye su, idan wannan siyasa ta sasantawa da Yahudawa ta yi nasara, to sai an wayi gari ta tarwatse ta koma wasu ‘yan kabilu da dauloli kamar ‘yan kaji. Da zarar haka ta faru kuwa, duk wani kokari na hada kan wannan al’umma, da bunkasa ta, da dora ta a kan godabe daya na rayuwa, zai ci tura.
  • Wannan sasantawa za ta takaita duk wani karfi da hadin kai, da al’ummar musulmi suke da shi, tare da canja mata tunani game da akidarta ta kokarin samar da cikakken tsaro ta fuskar soja. Sai kawai a wayi gari wannan siyasa ta karkatar da akalar wadancan tsare-tsare; al’ummar ta koma wasu ‘yan kasashe, da za a biyowa ana yi musu dauki daya-daya ana mamayewa ana kuma lakumewa.
  • Idan wannan sasantawa ta tabbata, to, al’ummar musulmi za ta fuskanci barazanar bacewa daga bayan kasa kwata-kwata. Ba abin da zai hana hakan faruwa, tunda sasantawar za ta canza salon rayuwar musulmi ne gaba dayansa; akidu da al’adu da alkiblarsu gaba daya za ta dauki sabon salo. A haka ba za su sake iya tayar da zancen gwagwarmaya da neman ‘yanci ba.
  • Yarda da wannan sasantawa da Yahudawa zai zama wani nau’i na mika wuya da yarda da an ci al’ummar musulmi da yaki. Har kuma an yarda an kuma amince da girma da daukaka da zaman Yahudawa madaukaka ta fuskar halaye da dabi’u da ilimi da kuma wayewa. Karshen hakan zai zama wani sanadin da wannan al’umma ta musulmi za ta yanke kauna sakamakon karayar tattalin arzikin tunani da kasa a guiwa.
  • Sasantawar nan da Yahudawa, zai gurbata tarihi, ya dasa itaciyar algussu a cikin kwakwalen mutane, kayan gadon ilimi da wayewa na Larabawa da sauran al’ummar musulmi, a rasa gane kai balle gindinsu.

Nauyin da Yake Kanmu:

  • Tabbas! kalubalantar wannan shiri na sasantawa nauyi ne da Shari’a ta dora wa kowane mutum duk inda yake a bayan kasa a matsayinsa na dan Adam, wanda kuma za a tambaye shi a kansa ranar Kiyama. Babu wani rukuni babba ko karami, daga cikin al’ummar musulmi da Larabawa da sauran masu hankoron kare hakkin dan Adam, a matakin daidaiku ko na  kungiyoyi da cibiyoyi komai yawansu face wannan nauyi yana a kan su; suna kuma da wata muhimmiyar rawa da za su taka, wadda za ta yi tasiri na a-zo-a-gani a cikin hana wannan shiri na sasantawa da Yahudawa tabbata.
  • Sa’annan kuma ya zama wajibi a kan malaman wannan al’umma, duk inda suke, su fito fili karara, su bayyana wa duniya matsayi da hukuncin wannan sasatanwa da ake shirin yi da Yahudawa. Kin yin haka kuwa wani nau’i ne na boye ilimi.
  • Duk wani malami mai tsoron Allah, ya zama wajibi a kan sa, duk kalmomin da za su fito daga bakinsa su kasance masu zafi da karfin da za su iya ruguza wannan sasantawa da sunan samar da sulhu da zaman lafiya.
  • Kalubalantar shiraruwan Yahudawa da yin nesa-nesa da duk wata yarjejeniya da kulla alkawurran aminci da su, wajibi ne a kan hukumomi da shugabanni domin bayar da kariya ga akidar al’ummar musulmi da Shari’a da kuma wuraren ibadarta masu tsarki.
  •  Su kuwa alkalai da sauran hukumomin Shari’a da kungiyoyinta na kare hakkoka, ya zama wajibi a kan su, wajabci irin na Shari’a da doka, su bayyana wannan shiri na sasantawa da Yahudawa a matsayin wani ta’addanci da ketare iyaka.
  • Kungiyoyin Musulunci da wadanda ba su ba kuma, da jam’iyyun siyasa, wajibi ne a kan su, su jagoranci shiraruwan kalubalantar wannan shiri na sasantawa da Yahudawa, ta hanyar duk da suke da iko, a matakin wakilci ko na ba hure ba kunne.
  • Su kuma manyan malamai irin wadanda Allah ya ba kaifin hankali da basira da wayewa irin na a-zo-a-gani, da ‘yan jarida da sauran masu tsayayyar magana, a matakin daidaiku da kungiyoyi, wajibi ne a kansu su tona ma wannan shiri na sasantawa da Yahudawa da masu kulle-kullen tabbatar da shi, asiri. Sa’annan su wayar da kan gaba dayan al’umma, domin ta kalubalanci wannan shiri, da kalima daya.
  • Wajibi ne babba a kan al’ummar musulmi da Larabawa su hana wannan kungiya ta Yahudawa saháyináwa ci gaba da wanzuwa tare da kakkabe hannuwansu daga ba ta kowace irin gudunmawa.
  • Su kuwa matasa ya zama wajibi a kan su, su zama gaba-gaba a cikin duk wani shiri na kalubalantar wannan yunkuri na sasantawa da Yahudawa, ta hanyar amfani da duk wani mataki da ya dace da hakan.
  • Wajibi ne kuma a kan mata musulmi, su hadu su yi magana da kalima daya, tare da nuna rashin amincewarsu da wannan shiri, domin kare mutunci da alfarmar al’ummar musulmi da wuraren ibadarsu masu tsarki.
  • Wajibi ne kuma a kan iyaye musulmi da sauran hukumomin ilimi da bayar da shi, su tarbiyanci yara tare da renon su a kan akidar rashin amincewa da wannan shiri na sasantawa da Yahudawa da kokarin ganin baya gare shi.      

قد يعجبك أيضاً

نشاطات في مختلف دول العالم دعما لـ”أسبوع القدس العالمي”

شهد اليوم الثاني من “أسبوع القدس العالمي”، نشاطات كثيفة في مختلف الدول العربية والإسلامية. في العراق، أعلن مسؤول لجنة العلاقات والإعلام في مجلس علماء العراق، د. محمد الفيصل، الجميع إلى المشاركة في “أسبوع القدس العالمي”، قائلا إن المجلس سينظم فعاليات عديدة خلال الأيام المقبلة. بدوره، قال مساعد الأمين العام في مجلس علماء العراق، د. يحيى […]

إغلاق فيسبوك أسبوع القدس

استمراراً وتمادياً في محاربة الحق الفلسطيني، وبعد النجاح والدعم الكبير الذي لاقاه أسبوع القدس العالمي من أبناء الأمة قامت إدارة فيسبوك بإغلاق صفحة الأسبوع على منصتها بحجة عدم اتباع معايير مجتمع فيسبوك، ولا يخفى استهداف إدارة فيسبوك للمحتوى الفلسطيني المتزايد في السنوات الأخيرة، بهدف كتم صوت الحقيقة الذي يحقّق أهم ركائز حقّنا الفلسطيني، وإن هذا […]

افتتاح فعاليات أسبوع القدس العالمي في ماليزيا

نظمت المؤسسات والروابط والهيئات الماليزية، أمس الجمعة، حفل الافتتاح الرسمي لأسبوع القدس العالمي لعام ١٤٤٣هـ، في ولاية ترنجانو الماليزية. وشهد الحفل حضور أعداد كبيرة من المشاركين، بالرغم من الهطول الكثيف للأمطار، وجرت فقرات الحفل كما هو مخطط له، في ميدان مسجد تنكو تنغه زهرة (المشهور بالمسجد العائم) الواقع بمنطقة كوالا إيباي. وافتتح الحفل عضو حكومة […]